Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Amince Da Naɗa Masu Bayar Da Shawara 20 Ga Tinubu

Majalisar dattawa ta amince da naɗin mutane 20 da shugaba
Tinubu ya aike mata domin amincewa da su a matsayin
mashawartan sa.

Matakin dai ya na zuwa ne, bayan da shugaba Tinubu ya aike wa majalisar wasiƙar neman amincewa domin ya naɗa mutanen.

Sai dai a wasiƙar da shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya karanto babu sunayen mutanen a ciki.

Ana dai kallon sabbin naɗe-naɗen da shugaba Tinubu zai yi a matsayin wata manuniyar inda alƙiblar gwamnatin shi za ta fuskanta wajen magance tarin matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.

Exit mobile version