Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Likitocin Najeriya Sun Soki Sabon Ƙudurin Majalisar Wakilan Ƙasa

Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Nijeriya, ta soki
ƙudurin da Majalisar wakilai ta gabatar, wanda ke neman
tilasta wa likitoci aikin shekaru biyar kafin samun lasisi.

Kungiyar ta bayyana adawarta ga ƙudurin ne, a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan wani taron gaugawa na shugabannin ta.

Sanarwar, ta ce ƙungiyar ta yi mamaki game da wanda ya gabatar da ƙudurin wato dan majalisa Ganiyu Johnson.

Haka kuma, kungiyar ta bayyana damuwa a kan rashin biyan albashi da ta ce gwamnatin tarraya ba ta yi ma wasu daga cikin ‘ya’yan ta ba, yayin da wa’adin gwamnatin ke zuwa ƙarshe.

Ta ce ta damu a kan yunƙurin majalisar wakilai na tilasta wa likitoci abin da ta kira da ‘karin zangon shekaru biyar bayan karatun digiri kafin a ba su lasisi, ko a bar su su fita zuwa ƙasashen waje idan su na da sha’awar yin hakan.

Exit mobile version