Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kwamitin Amintattun PDP Ya Dage Kan Sashin Arewa Ta Tsakiya

PDP (1)

PDP (1)

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya yi kira ga masu ruwa da tsaki daga shiyyar arewa ta tsakiya su gaggauta fitar da sabon shugaban jam’iyyar na kasa domin maye gurbin Sanata Iyorchia Ayu.

An cimma matsayar ne a taron da kwamitin ya gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja a wani gagarumin yunkuri na mayar da babbar jam’iyyar adawa ta koma kan turba.

Wannan kudiri wanda yana cikin jerin umarnin da aka fitar yayin wani taron gaggawa ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan halin da jam’iyyar ke ciki.

Da yake karanta sanarwar, shugaban kwamitin amintattun PDP, Sanata Adolphus Wabara ya bayyana matukar damuwar sa kan shugabannin jam’iyyar na rigingimun cikin gida da ake fama da su,

Da kuma jinkirin warware muhimman batutuwan jam’iyyar.

Kwamitin amintattun ya bayyana matukar damuwa game da halin da PDP ke ciki, musamman game da tsarin gudanarwa da yanke shawara na kwamitin zartarwa na jam’iyyar.

Ya bukaci kwamitin zartarwa da ya gaggauta daukar matakin maido da jituwa cikin gida, da hadin kai, da amincewar jama’a ta hanyar bin kundin tsarin mulkin PDP, gami da bin tsarin karba-karba na mukaman jam’iyyaar ga dukkan sassan kasa.

Exit mobile version