Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kuncin Rayuwa: Wasu Matasa Sun Fasa Rumbun Abincin Gwamnati A Jihar Kebbi

Waɗansu mutane da kawo yanzu ba a bayyana kama ko ɗaya
daga cikinsu ba sun fasa rumbun abincin gwamnati a Jihar
Kebbi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an fasa rumbun abincin da ke Unguwar Bayan Kara a Birnin Kebbi a jiya Lahadi, Mutanen da suka fasa rumbun sun fi galaba ne a kan jami’an tsaron da aka ɗora wa alhakin tsare rumbun da gwamnati ta shake da kayan abinci.


An bayyana cewa bayan Rumbun Gwamnati da aka fasa,  mutanen sun wawushe kayan abincin da ke makare a wata mota da ta lalace a kan hanya.


Shugaban ’yan kasuwar Bayan Kara dake Birnin Kebbi Muhammadu Gwadangwaji ya ce, ba iya Rumbun Gwamnati mutane suka fasa ba.


A cewarsa, an fasa wasu shagunan ’yan kasuwa an kuma cinna wa wasu wuta, duk da irin ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris; Ahmed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici

Exit mobile version