Gwamnatin tarayya ta bayyana kudirin ta na ciwo bashin cikin gida da na waje har naira tiriliyan 4 da biliyan 89, domin samar da kudaden kasafin shekara ta 2022 na naira tiriliyan 5 da biliyan 62.
Ministar kudi da kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin tarayya za ta rage yawan kudaden da ta ke narka wa ma’aikatu da hukumomi da ya kai naira biliyan 259 da miliyan 31.
Zainab Ahmed, ta kuma bayyana yadda gibin da za a shiga da shi shekara ta 2022 na naira tiriliyan 5 da biliyan 62 ya karu da sama da naira tiriliyan 5 da biliyan 60 a shekara ta 2021.
Ministar, ta ce za a yi amfani da kudin da za a ranto daga ciki da wajen Nijeriya wajen cike gibin da aka samu ne.