Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu Ta Umarci Aa Zaura Ya Gurfana A Gabanta Kan Zargin Rashawa

Wata babbar kotu tarayya da ke zama a Kano ta umarci ɗan takarar sanata na Kano Ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar APC Abdulsalam Abdulkarim-Zaura, ya gurfana a gaban ta bisa zargin rashawar Dala miliyan 1 da dubu 300

Hukumar EFCC ce ta shigar da kara a kan A.A Zaura, bayan an zarge shi da samun kuɗaɗen ta hanyar da ba ta dace ba.

Alkalin kotun Muhammad Nasir-Yunusa da ya bukaci Zaura ya gurfana a gaban sa, ya bada umarnin ne bayan sauraren karar da aka shigar a kan dan takarar.

Mai shari’a Nasir Yunusa, ya ce dole ne a ji daga bakin AA Zaura kafin a dauki mataki na gaba.

Exit mobile version