Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kasuwanci : Dangote Yana Neman Kafa Matatar Mai Na Legas A London

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote na shirin
kafa wata kungiyar hada-hadar man fetur, mai yiwuwa a birnin
Landan.


Ya dauki matakin ne domin taimakawa wajen samar da danyen mai da kayayyakin da za a samar da sabuwar matatarsa a Najeriya, kamar yadda wasu majiyoyi shida da ke da masaniya kan lamarin suka bayyana.


Matakin dai zai rage rawar da manyan kamfanonin kasuwanci na duniya ke takawa, wadanda suka shafe watanni suna tattaunawa don samar wa matatar kudade da danyen mai a madadin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare.


Katafariyar matatar mai, mai hakar kimanin ganga 650,000 a kowace rana na shirin sake hako mai a duniya kuma ‘yan
kasuwa na sa ido sosai kan yadda za ta gudanar da ayyukanta.


Dangote, wanda mujallar Forbes ta kiyasta dukiyarsa akan dala biliyan 12.7, bai bada amsa kan wasu bukatu da yawa ko sharhi ba.

Exit mobile version