Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kasar Saudiyya Ta Daƙile Harin Da Houthi Ta Kai Filin Jirgin Abha

Houthi Attack Saudi

Rundunar sojin Saudiyya ta ce ta daƙile wani harin jirgi marar matuƙi da ƴan tawayen Houthi suka ƙaddamar a Yemen.

Saudiyya tayi zargin cewa an kai harin ne da nufin lalata filin jirgin sama na Abha.

A yayin harin Mutum huɗu sun ji rauni sakamakon tarkacen jirgin da ya fado daga sama.

Tuni dai ‘Ƴan tawayen suka ci gaba da kai hare-hare kan iyakokin ƙasashen biyu.

Inda Suka ce suna mayar da martani ne kan hare-haren saman da rundunar sojin haɗakan da Saudiyya ke jagoranta ke kai wa a yankunan da mayaƙan Houthin ke iko da su.

Exit mobile version