Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Karramawa: Buhari Zai Karbi Lambar Yabo Kan Zaman Lafiya a Mauritaniya


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai karbi kyautar “Karfafa zaman lafiya ta Afirka” a birnin Nouakchott na kasar Mauritaniya.

Kakakin Shugaban, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce Buharin zai karbi kyautar ce saboda irin rawar da yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya da kuma yin sulhu a kasashe daban-daban na Afirka.
Kwamitin Zaman Lafiya na Abu Dhabi, ne dai zai gabatar wa Buhari kyautar.
An kafa kwamitin na Shugabannin Kasashe ne a shakara ta 2014 domin a lalubo hanyoyin bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya.
Adesina ya kuma ce gabanin Buharin ya karbi kyautar, Shugaban zai halarci taron kasashen Afirka kan samar da zaman lafiya, inda zai gabatar da makala a wajen taron.
Kakakin ya ce Buhari zai bar Najeriya ne ranar Litinin din nan, inda ake sa ran dawowarsa ranar Laraba.
Daga cikin wadanda zasu yiwa Buhari Rakiya sun hada da ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da na Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi da mai ba shi shawara an tsaro, Babagana Monguno, da Shugaban Hukumar Leken Asiri, Ahmed Rufai Abubakar

Exit mobile version