Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kara Harajin Kaya Zai Jefa Rayuwar Talaka Cikin Mawuyacin Hali – Ndume

Ndume Ya Ce Kara Harajin Kaya Zai Jefa Rayuwar Talaka Cikin Mawuyacin Hali

Ndume Ya Ce Kara Harajin Kaya Zai Jefa Rayuwar Talaka Cikin Mawuyacin Hali

Dan majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Muhammad Ali Ndume ya shawarci gwamnati game da yunkurinta na kara harajin kaya domin samun karin kudi yana mai cewa a maimakon haka, kamata ya yi gwamnatin ta bijiro da tsarin karbar haraji daga masu amfani da waya.

Sanata Ndume ya ce idan har gwamnati ta aiwatar da Karin harajin kaya, toh kuwa talaka ne zai shiga halin ni-‘ya-su ta yadda farashin komai a kasuwa zai daga kama daga farashin mai da magani da mota da abinci.

Sanatan mai wakiltar Borno ta kudu a zauren majalisar dattawan ya bayar da misali da kasar Ghana da ita ma cikin 2008 ta samar da tsarin kara haraji ga masu amfani da waya inda masu amfani da wayar ke biyan kashi shida, a baya-bayan nan kuma, suna biyan kashi tara cikin dari.

Ya ce bayan da gwamnatin Ghanar ta samar da wannan tsari, ta rage harajin kaya saboda talaka ya samu sauki ta wata fuskar. A cewar Ndume, mutane kusan miliyan 60 ne suke amfani da waya a Najeriya wanda a ganinsa, wannan ce hanya mafi sauki da gwamnati za ta tara kudade

Exit mobile version