Da safiyar yau Talata gamayyar kungiyoyin ma’aikatan da ke aiki a bangaren sufurin jirgin sama na kasa, suka janye yajin aikin da suka shirya yi a fadin kasar.
Kungiyoyin sun fasa daukar matakin ne bayan da suka rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da gwamnatin tarayya, yayin wani zama na musamman da aka yi a shalkwatar ma’aikatar kwadago ta Najeriya a ranar Litinin a Abuja.
Manyan batutuwan da suka janyo barazanar yajin aikin sun hada da rashin biyan ma’aikata sabon albashi mafi kankanta, wanda tun 2019 ya kamata a fara biya.
Batu na biyu kuma shi ne jinkirin fara amfani da sharuddan aiki kamar yadda suka shafi ma’aikatan da ke aiki a hukumomin gwamnatin tarayyar.
Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya tabbatar da kulla yarjejeniyar inda ya bayyana cewa sun yarda tsakanin su cewa hukumar da ke tsara albashin ma’aikata ta kasa za ta aika wa dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya – har da wadanda ba ma’aikatan gwamnati ne ba – wata wasika da ke fayyace matakan da ya dace su dauka kan biyan albashin ma’aikata karkashin dokar Albashi ta bai daya na 2019.

