Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zanga A Lagos

Jami’an tsaro na musamman da aka girke a jihar Lagos, sun tarwatsa dandazon masu zanga-zangar juyin-juya hali da su ka yi wa suna ‘RevlutionNow’ a Turance, wadanda su ka taru tunda safiyar Litinin din nan domin nuna adawa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Tun da sanyin safiya ne aka girke jami’an tsaron a babban filin wasa na Surulere, inda a nan ne aka tsara haduwar masu zanga-zangar da gwamnati ke zargin wasu tsirarun ‘yan adawa da kitsawa, da nufin kara janyo rudani baya ga matsalolin tsaro da ake fuskanta.

Wasu ganau sun shaida yadda jami’an tsaron su ka rika harba Borkonon-Tsohuwa a kan dandazon masu zanga-zangar, sai dai har yanzu babu rahoton jikkata ko rasa rai sakamakon arangamar.

Tun ranar Asabar da ta gabata ne, Rundunar ‘yan sanda ta gargadi masu zanga-zangar, tare da barazanar ayyana duk wanda ya shiga gangamin a matsayin dan ta’adda, baya ga daukar matakin kama jagoran zanga-zangar Omoyele Sowore a daren Juma’ar da ta gabata.

Exit mobile version