Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

INEC Ta Kwantar Da Hankalin Jama’a, Tace Murde Zaben 2023 Ba Zai Yiwu Ba

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba za ta yiwu a yi cuwa-cuwa wajen tattara sakamakon zabe ba.

Farfesa Mohammad Kuna ya bayyana haka, a wajen wani taro da Kwamitin wanzar da zama lafiya a karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar, da kuma cibiyar Kukah su ka shirya a Abuja.

Yayin taron na kara wa juna sani, an tattauna a kan irin gudumuwar da fasahar zamani za ta bada wajen gudanar da zabe.

Mai bada shawara na musamman ga shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mohammad Kuna, ya ce da zarar malaman zabe sun yi amfani da na’urar da su ka tura sakamakon kuri’un da aka kada a rumfa magana ta kare.

Na’urar da aka zo da ita dai ta na amfani wajen tantance katin zabe da kuma mai kada kuri’a, kuma ba za ta bari wani ya kada kuri’a da katin wani ba, don haka ba za ta yiwu a murde sakamakon zabubbukan da aka dora ba.

Exit mobile version