Tsohon Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin
tarayya Abubakar Malami, ya musanta zargin cewa ya gudu
saboda zargin rashin gaskiya.
An dai sha yada jita-jitar cewa tsohon Ministan ya fice daga Nijeriya, amma ya karyata labarin.
Jita-jitar dai ta yi Kamari ne bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a dakatar da shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa.
Abubakar Malami dai ya rike matsayin Lauyan gwamnatin tarayya na tsawon shekaru takwas a mulkin Muhammadu Buhari, wanda ake tunanin shi ne ya shiga ya fita har Abdulrasheed Bawa ya samu shugabancin hukumar EFCC, Zargin da ya karyata tun ya na kan tsohuwar kujerar sa.

