Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Har Yanzu Shekarau Ne Dan Takarar Nnpp A Kano Ta Tsakiya – INEC

Hukumar Zabe mai zaman kan ta ta Kasa INEC, ta ce har yanzu tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau ne dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar NNPP.

Tun ranar 29 ga watan Agusta na shekara ta 2022, Shekarau ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar PDP, amma hukumar zaben ta fitar da sunan sa a matsayin dan takarar jam’iyyar NNPP.

Ganin sunan Shekarau a matsayin dan takarar Kano ta Tsakiya na jam’iyyar NNPP dai ya janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa.

Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kai na hukumar zabe Festus Okoye, ya tababtar da cewa har yanzu Sanata Ibrahim Shekarau ne dan takarar jam’iyyar NNPP.

Ya ce Jadawalin zaben da su ka fitar a ranar 26 ga watan Fabrairu, ya sanya 15 ga watan Yuli a matsayin ranar karshe ta janyewa daga takara ko sauya dan takarar Majalisar Dokoki ta Tarayya, kuma Shekarau bai tashi janye takarar sa ba sai ranar 26 ga watan Agusta na shekara ta 2022.

Exit mobile version