Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce akwai alaka tsakanin talauci da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a Nijeriya, domin idan bambanci tsakanin masu kudi da talakawa ya karu sai rashin zaman lafiya ma ya karu.
Ya ce za su iya fitar da mutane miliyan 100 daga talauci a cikin shekaru 10 idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata.
Shugaba Buhari, wanda ya fara wa’adi na biyu a kan karagar mulki a karshen watan Mayu, an zabe shi ne bisa alkawarin samar da zaman lafiya da yaki da cin hanci da rashawa.
Sai dai yayin da aka samu raguwar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa, an kuma samu karuwar sace-sacen jama’a da hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan Nijeriya.
Game da ikirarin cewa za su iya fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talauci, wani masanin tattalin arziki Abubakar Aliyu ya ce zance ne kawai, domin a yanzu babu wani tsari a kasa da zai nuna cewa hakan mai yiwuwa ne, don haka ya akalanta hakan a matsayin kalamai ne kawai irin na ‘yan siyasa.