Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Har Yanzu Ana Fama Da Talauci A Nijeriya – Oshiomole

Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur

Adams Oshiomhole, Shugaban Jam’iyyar APC Ta Kasa

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Adams Oshiomhole, ya ce har yanzu akwai hauhawar matsanancin talauci a fadin Nijeriya, duk kuwa da cewa tattalin arziki ya karu.

Oshiomhole ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen taron Nazari Da Bitar Alkawurran Da jam’iyyar APC Ta dauka a lokacin yakin neman zabe daga shekara ta 2015 zuwa yau.

Taron, wanda ya gudana a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, ya samu halartar jiga-jigan gwamnati da su ka hada da Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnoni da sauran su.

Oshiomhole ya ce ko shakka babu, gwamnatin shugaba Buhari ta yi rawar gani wajen kawo ci-gaba a Nijeriya, musamman idan aka dubi alkawurran da ta cika.

Sai dai ya ce har yanzu dimbin jama’a su na fama da manatsanancin talauci da kuncin rayuwa, ya na mai cewa akwai bukatar bankuna su kara himma wajen bada kananan basussuka ga matsakaitan ‘yan kasuwa domin tattalin arziki ya inganta.

Exit mobile version