Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnati Ta Nemi Daliban Nijeriya Su Zauna A Gida Kafin A Zo A Kwashe Su

Gwamnatin tarayya, ta sake nanata kudirin ta na cewa daliban Nijeriya da ke kasar Sudan su kasance a masaukan su, yayin da ta ke ci-gaba da shirye-shiryen kwaso su.

Gwamnatin tarayya, ta sake nanata kudirin ta na cewa daliban Nijeriya da ke kasar Sudan su kasance a masaukan su, yayin da ta ke ci-gaba da shirye-shiryen kwaso su.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Nijeriya ta fitar, ta shawarci daliban su yi watsi da sanarwar da kungiyar dalibai ta kasa ta sanar, inda ta yi kira ga daliban su hadu a Jami’ar Kasa da Kasa ta Afirka, da ofishin kungiyar dalibai da kuma Jami’ar El-Razi, domin a kwashe su sannan su riko dala 100 ko 200.

Kamar yadda ofishin jakadanci ya sanar tun da farko, ana rokon daliban su kwantar da hankalin su, su kuma kasance a masaukan su yayin da ofishin ke ci-gaba da shirye-shirye domin fara jigila.

Sanarwar ta kara da cewa, Ofishin Jakadancin ya na so ya tabbatar wa daliban Nijeriya cewa lafiyar su ita ce abu mafi mahimmanci.

Exit mobile version