Tsohon ministan Neja Delta a zamanin Mulkin Goodluck Jonathan Godwill Orubebe ya fice daga Jam’iyyar PDP.
Orubebe dai shi ne mutumin da ya so ya tada hatsaniya a lokacin da ake bayyana sakamakon zaben shugaban kasa na shekara ta 2015, wanda shugab Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya yi nasara.
A cikin wata wasika da ya aike wa Jam’iyyar PDP a yankin karamar hukumar Burutu ta jihar Delta ne ya ayyana ficewar sa daga PDP, sai dai bai bayyana Jam’iyyar da zai koma ba, amma ana raderadin cewa zai koma Jam’iyyar APC ne.
Orubebe dai ya yi suna a lokacin zaɓen shekara ta 2015, musamman yadda ya tada ballin cewa sai an soke zaɓen a daidai lokacin Farfesa Attahiru Jega ya ke bayyana sakamakon zaɓen a Abuja, inda da kyar aka shawo kan sa har aka iya kammala bayyana sakamakon zaɓen.
Ana kyautata zaton cewa, Orubebe bai amince da zaɓin gwamnan jihar Delta Okowa da Atiku Abubakar ya yi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa ba.

