Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Garkuwa Da Mutane: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya

Majalisar dattawa ta bukaci shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammadu Adamu ya bayyana gaban ta, domin jin ta bakin sa game da yadda ta’addancin masu garkuwa da Mutane ke ci-gaba da kamari a fadin Nijeriya.

An dai gayyaci Muhammadu Adamu ne domin samun masaniya tare da kulla dabaru da shawarwarin kawo karshen ta’addancin garkuwa da mutane a Nijeriya.

Majalisar, ta yanke shawarar gayyatar shugaban ‘yan sandan ne, biyo bayan kudirin da Sanata Shehu Sani ya gabatar.

Bayan tattaunawa a kan batutuwan ta’addancin masu garkuwa da mutane, musamman a yankunan jihar Kaduna, majalisar ta yanke shawarar gayyatar shugaban ‘yan sandan domin daura damarar dasa aya a kan wannan mummunan kalubale.

Yayin tafka muhawara a zauren majalisar, Sanata Shehu Sani ya ce, ta’addancin masu garkuwa da kashe-kashen al’umma baya ga kone gidaje a wasu kauyukan jihar Kaduna, ya kai intaha da kawo yanzu an gaza gane bakin zaren.

Exit mobile version