Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Matakan Tsaro: Buhari Ya Umurci Shugabannin Tsaro Su Yi Aikin Ba Sani Ba Sabo

Rahotanni na cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci hukumomin tsaro cewa kada su rangwanta wa duk masu haifar da ta’addanci a jihar Zamfara da kewayen ta da ma sauran sassan Nijeriya.

Shugaban ma’aikatan tsaro na kasa Janar Gabriel Olanisakin ya bayyana wa manema labarai haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jim kadan bayan ganawar su da ta tsawon sa’o’i biyu da shugaba Buhari.

Da yak e bada rahoton matakan tsaron da hukumar ‘yan sanda ta dauka, mukaddashin shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muhammadu Adamu, ya ce a halin yanzu hanyar Abuja zuwa Kaduna ta tsarkaka daga ta’addancin masu garkuwa da mutane.

Exit mobile version