Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gargadi: Laifi Ne Babba Biyan Kudin Gyara Na’Ura Ta Tranfoma- Jed

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JED) ya shawarci
abokan huldarsa a Jihar Gombe da kada su biya kowa kudin
gyara na’urar taransfoma a yankunansu.


Babban jami’in tsaro na JED, Musa Abdullahi, ya ce, ba hakkin kwastomomi ba ne su gyara taransfoma idan ta lalace.


Abdullahi ya ce ana sa ran jama’a su kai rahoto ofishin JED mafi kusa a duk lokacin da na’urar taransifoma ta samu matsala, kuma kada su biya wani jami’inta kudin gyara.


Ya ce ba daidai ba ne a nemi al’umma su ba da gudummawar kudi don gyara ko canza taransfomarsu da ta lalace, hasali ma
yaudara ce da kamfanin ba zai lamunta ba.


Jami’in ya shawarci al’ummar jiha da su kai rahoton duk wani ma’aikacinsu da ya nuna irin wannan bukata domin daukar matakin da ya dace.

Exit mobile version