Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Fasa Bututu: NNPC Ya Ce An Saci Danyen Man Najeriya Sau 240 A Mako Guda

Kamfanin Man Fetur na Najeiya NNPCL ya ce sau 240 barayi suka fasa butun danyen mai a sassan Najeriya a cikin mako guda da ya gabata.

Kamafnin na NNPCL ya ce fasa bututu da satar danyen mai sun kara kamari ne a yankin Neja Delta musamman jihohin Ribas da  Bayelsa da Delta, inda aka gano aka kuma toshe wurare 93 da barayin suka jona bututu suna satar mai daga bututun gwamnati.

Kamfanin da jami’an tsaro sun ce sun kuma gano wurare 27 da barayin suka fasa bututun domin kwasar danyen mai, wanda a halin yanzu kamfanin ke aikin gyaran su.

Wata sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce duk da cewa an gano tare da lalata haramtattun matatun mai 69 a cikin wata guda da ya gabata, matsalar tsaro a bangaren danyen mai zai kawo karin koma-baya ga tattalin arzikin Najeriya.

Sanarwar ta ce a mako guda da ya gabata, an kama akalla jiragen ruwa na katako guda 30 da manyan motoci da ake amfani da su wajen safarar man sata da dai sauran laifuka.

Sai da kuma kamfanin bai ambaci komai game da matakin da aka dauka a kan mutanen da ke da alaka da jiragen da kuma haramtattun matatun ba.

Exit mobile version