Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Farashin Mai: An Kara Kudin Fetur Daga Naira 165 A Hukumance

Gwamnatin Tarayya ta kara farashin Mai zuwa fiye da Naira 165 a hukumance.


Duk da cewa a baya akan sayar da man a wasu gidajen mai akan fiye da hakan, a ranar Talata ne aka tabbatar da farashin a hukumance.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Jadawalin kafin farashin da ya fara aiki ya nuna za a rika sayar da man fetur akan Naira N184 zuwa N189 a yankin arewa maso yamma da Arewa maso gabashin Najeriya, inda aka Kara Naira 24.

A yankin Arewa ta tsakiya kuma za a rika sayar da litar man akan Naira 179, yankun Kudanci kuma N165 zuwa N179 ko da yake ana sayarwa N169 a Legas, yayinda a Abuja ake sayarwa akan Naira 174 kowace lita.


An kuma kara farashin daga a gidajen mai da ke yankin Legas daga N148.17 zuwa daga N160 zuwa 162.


Manyan rumubunan mai a yankin Warri/Ogbarra sun kara farashinsu zuwa tsakanin N162 da N165 a Fatakwal kuma an kara zuwa tsakanin N165 zuwa N167.


Dillalan man fetur sun ce Gwamnatin Tarayya ta sahale musu karin farashin, saia dai duk kokarin da aka yi na jin ta bakin kakakin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur, Apollo Kimchi, ya ci tura.

Exit mobile version