Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Fahari: Babu Wanda Zai Iya Yin Takara Da Bola Tinubu A Shekara Ta 2023 – Sanata

Jigo a jam’iyyar APC Sanata Abu Ibrahim, ya ce babu wani dan takara daga kudancin Nijeriya da zai iya ja da Bola Ahmed Tinubu a zaben shekara ta 2023.

Jigo a jam’iyyar APC Sanata Abu Ibrahim, ya ce babu wani dan takara daga kudancin Nijeriya da zai iya ja da Bola Ahmed Tinubu a zaben shekara ta 2023.

Sanata Ibrahim, ce wadanda ake ganin za su nemi shugabancin Nijeriya a yankin kudu maso yamma ‘yan’uwan Tinubu ne kuma ba za su yi takara da shi ba.

Ya ce Tinubu ya taka rawa wajen dawowar Kayode Fayemi a kan mulki karo na biyu, kuma shi ya dauko Osinbajo ya dora a kan kujerar mulki a shekara ta 2015.

Sanatan ya kara da cewa, lokaci ya yi da ya kamata a mara wa kudirin Tinubu baya domin ya taka gagarumar rawar a zo a gani.

Exit mobile version