Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

EFCC Ta Cafke Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saboda Karkata Naira Biliyan 22

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta kama tsohon
ministan wutar lantarki Injiniya Saleh Mamman, bisa zargin
karkatar da naira biliyan 22 da aka ware domin inganta samar
da wutar lantarki a fadin Nijeriya.

Rahotanni sun ruwaito cewa, jami’an hukumar EFCC sun yi awon gaba da tsohon ministan ne domin amsa tambayoyi a kan yadda wadannan makudan kudaden su ka salwanta.

Bayanai sun ce, ana zargin Saleh Mamman ne da karkatar da naira biliyan 22 da aka ware domin aikin samar da wutar Zungeru da Mambilla, wadanda ake zargin ministan ya raba tare da wasu manyan jami’an ma’aikatar sa.

Majiyoyi sun ce, jami’an EFCC sun yi nasarar gano wasu kadarori a Nijeriya da kasashen ketare, wadanda ministan ya mallaka tare da wasu tarin kudade da su ka kunshi nairori da dalolin Amurka.

Exit mobile version