Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, sun kama wani kasurgumin mai safarar kwayoyi, wanda aka danganta da shigo da kwayar Tramadol da kudin sa ya kai Naira biliyan 3, lamarin da ya jefa DCP Abba Kyari cikin matsala.
Kakakin hukumar NDLEA Femi Babafemi ya shaida wa manema labarai cewa, bayan watannin da aka shafe ana tattara bayanan sirri, jami’an hukumar sun kama shugaban rukunin kamfanonin Mallinson Emmanuel Ukatu, cikin wani jirgin sama a filin tashi da saukar jiragen sama na Abuja yayin da ya ke kokarin tserewa.
Babafemi ya ce, bincike ya nuna cewa Chief Mallinson, wanda ya Mallaki kamfanonin harhada magunguna da na sarrafa robobi, ya na dodorido da su ne don shigowa da haramtattun kwayoyi, sannan attajirin ya mallaki asusun ajiyar banki har guda 103 da ya ke amfani da su wajen halasta kudaden haram.
Ya ce bayan an kama wani ma’aikacin Ukatu tare da wasu yaran Abba Kyari, ya jagoranci ma’aikata zuwa wani gidan ajiye kaya na Mallinson da ke unguwar Ojota a Lagos, inda aka samu karin kwalayen kwayar Tramadol guda 197, wadanda aka yi kiyasin kudin su ya kai Naira biliyan 3.

