Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Daraja: CBN Ya Musanta Jita-Jitar Karya Naira Naira Zuwa 631 Kan Dala Guda

Babban bankin Najeriya CBN ya musanta rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, wanda ya bayyana cewar ya rage darajar Naira zuwa 631 akan kowace dala guda, daga ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2023.

Sanarwar da darakatan yada labaran babban bankin CBN Isa Abdulmumin ya fitar, ta ce ko kadan babu gaskiya a cikin rahoton, wanda ga dukkan alamu an so yin amfani da  shi ne wajen haifar da rudani, sakamakon rashin sanin da yake damun kafar  yada labaran da ta wallafa rahoton.

Babban bankin na Najeriyar ya kara da cewar darajar dala akan kowace Naira na nan akan 465 sabanin 631 da aka yada cewar shi ne sabon tsarin a canjin kudin da ya fara aiki a yanzu.

Sanarwar ta shawarci dukkanin kafafen yada labarai su rika tuntubar  babban bankin Najeriyar, domin tabbatar da hujjoji ko bayanan da suke neman amfani da su, musamman akan batun da ya shafi hada-hada ko canjin kudade.

Exit mobile version