Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dalilin Da Ya Sa Aka Hana Daukar Yara ‘Yan Kasa Da Shekara 12 A Makarantu

Gwamnatin tarayya, ta ce daga yanzu ba za a rika daukar yara ‘yan kasa da shekaru 12 a makarantun sakandare na gwamnatin tarayya ba, saboda a doka ba su kai su shiga makarantar Sakandare ba.

Babban sakataren ma’aikatar ilimi Andrew Adejoh ya sanar da haka, yayin da ake sa Ido a jarabawar shiga makarantun sakandaren gwamnatin tarayya.

Adejoh, ya ce gwamnati a shirye ta ke domin ganin an kiyaye wannan doka, saboda yin hakan zai taimaka wajen kawar da matsalolin da fannin ilimi ke fama da su a Nijeriya.

Ya ce ya ga yaran da ba su wuce shekaru 10 ba, inda uku daga cikin su ‘yan shekaru 9 ne sun shiga makarantar sakandare.

Exit mobile version