Annobar coronavirus ta kama mutum 873 a Najeriya bayan karin mutum 91 sun kamu da cutar a rana guda.
Cutar ta kashe mutum 28 a Najeriya inda wasu 648 ke kwance a asibiti, baya ga wasu mutum 197 da suka warke, ya zuwa karfe 11:25 na daren Laraba, 22 ga Afrilu, 2020.
Mutum 74 ne suka kamu da cutar a ranar Laraba a jihar Legas, inda cutar ta fi kamari.
Akwai kuma karin mutum 5 a Katsina, da wasu 4 a Ogun, a cewar Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC.
Cibiyar ta ce a jihar Delta an samu karin mutum 2, da kuma 2 a Edo. Akwai kuma mutum daya-daya a jihohin Kwara, Oyo, Adamawa da kuma Abuja.
Alkaluman COVID-19 da NCDC ta fitar sun nuna cewa a jihar Legas ce aka fi samun wadanda suka kamu da cutar a Najeriya da wayan mutum fiye da 504 da kuma sauran jihohin kamar haka:
- Lagos – 504
- Abuja -119
- Kano – 73
- Ogun – 24
- Katsina – 21
- Osun – 20
- Oyo – 17
- Edo – 17
- Kwara – 10
- Kaduna – 9
- Akwa-Ibom – 9
- Borno – 9
- Bauchi – 8
- Delta – 6
- Gombe – 5
- Ekiti – 4
- Ondo – 3
- Rivers – 3
- Jigawa – 2
- Enugu – 2
- Niger – 2
- Abia – 2
- Benue – 1
- Anambra – 1
- Sokoto – 1
- Adamawa-1
Hakan na zuwa ne washegarin ranar da mutum 117 suka maku da cutar a rana guda a kasar.