Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Cikin Makonni 2 Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Rushe Gine-Ginen Biliyan ₦126 A Kano

Wani rahoto ya nuna cewa, hankalin Jama’a da dama mazauna yankin unguwar Salanta da ke cikin birnin Kano ya tashi, yayin da mazauna unguwar su ka yi tir da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na ci-gaba da rusa wasu gine-gine da ake zargin sun saba wa doka.

Wuraren da gwamnatin Kano ta rushe dai sun hada da wani gini mai hawa uku mai dauke da shaguna sama da 90 a filin wasan tsere da keNasarawa, wanda kudin sa ya haura Naira biliyan 100, da masaukin baki na Daula mai dakuna 90 da ya lakume zunzurutun kudi sama da Naira biliyan 10.

Mutane da dama sun rasa wuraren sana’o’in su saboda rushe-rushen da aka yi, kuma ana ci-gaba da rushe wasu gine-ginen domin yin takunkumi ga abin da gwamnati ta kira mamaye filayen jama’a. Gwamnatin jihar Kano dai ta tabbatar da mutuwar mutane biyu da ta bayyana a matsayin masu kwasar ganima bayan an kaddamar da rushe-rushe

Exit mobile version