Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mun Kwato Filaye Na Tiriliyoyin Naira A KANO

Gwamnatin Jihar Kano, ta ce ta kwato filaye na tiriliyoyin naira tun bayan da Abba Kabir Yusuf ya karbi mulkin jihar.

Sabuwar gwamnatin Kano dai ta rushe gine-ginen da ke masaukin baki na Daula, da filin idi da kasuwannin Kwari da Wambai da dai sauran su, lamarin da ya haddasa cece-kuce a ciki da wajen jihar.

Gwamnatin Abba Kabir dai ta zargin tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da mamaye filaye ba bisa ka’ida ba, zargin da ta musanta tare da bayyana shi a matsayin maras tushe.

Sakataren gwamnatin jihar Dakta Baffa Bichi ya sanar cewa, darajar kudin gine-ginen da su ka rusa ta kai tiriliyoyin Naira yayin wata hirar sa da kafar talabijin ta Channels.

Ya ce sun kwato filayen da darajar su ta kai tiriliyoyin naira mallakin gwamnatin jihar Kano da tsohuwar gwamnati ta yi raba wa jami’an ta da iyalai, kuma Filin sallar idi kadai kudin sa ya kai tiriliyoyin naira.

Exit mobile version