Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ci Gaba: Lambar NIN Ta Wajaba Ga Masu Zana Jarrabawar WAEC A 2022

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Yammacin Afirka WAEC, ta ce za ta sanya bukatar lambar katin dan kasa ta NIN ya zama tilas ga masu zana jarrabawar a bana.

Jami’in hukumar ta kasa, Patrick Areghan ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Talata a Jihar Legas.

A cewarsa, hukuncin hakan ya biyo bayan umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar da tabbatar da kowane dan Najeriya ya mallaki katin shaidar dan kasa ta

Partrick ya ce, tuni hukumar WAEC ta bukaci dalibai da su mika lambar NIN dinsu ga hukumomin makarantun da za su zana jarrabawar a bana.

Hukumar ta ce daga shekarar 2022, sanya lambar NIN yayin rajistar jarrabawar zai zama wajibi ga kowane dalibi.

Exit mobile version