Hukumar Shirya Jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta
Yamma WAEC, ta sanar da cewa za a gudanar da jarrabawar
kammala Sakandare ta shekara ta 2023 tsakanin 8 ga watan
Mayu zuwa 23 ga watan Yuni.
Shugaban hukumar na ƙasa Patrick Areghan ya bayyana haka, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai gabanin jarrabawar a Legas.
Areghan, ya ce jarabawar za ta ƙunshi mutane Miliyan 1 da dubu 621 da 853 daga makarantun gwamnati da masu zaman kan su dubu 20 da 851.