Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Burkina Faso : Yan Ta’adda Sun Kashe Manyan Jami’an Sojin

OIP (3)

OIP (3)

Bayanai na cewa ƴan ta’adda sun farwa tawagar jami’an tsaron Burkina Faso, amma sai a wannan rana ne labarin faruwar lamarin ya fita.

sai dai kuma majiyoyi da dama daga rundunar tsaron ƙasar ta shaidawa sashen Faransanci na RFI cewa an sami asarar rayukan manyan jami’an tsaro a yayin wannan hari.

Bayanai sun ce baya ga asarar rayuka ƴan ta’addar sun tsere da manyan makamai da kuma tankokin yaƙi yayin fafatawar.

Wasu ƙarin bayanai da suka fayyace yadda lamarin ya faru,

sun ce ƴan ta’addar sun yiwa sojojin kwanton ɓauna ne a kan hanyar da ta tashi tsakanin Ougarou da Boungou da ke gabashin ƙasar,

hanyar da aka daina amfani da ita tun watan Nuwambar 2019, a sakamakon wani ƙazamin hari da aka kai kan masu haƙar ma’adanai.

Kai hari akan wannan hanya ba wani sabon abu bane, la’akari da yadda a baya ƴan ta’addar suka sha yiwa matafiya daga jami’an tsaro kwanton ɓauna suna kashe su.

Exit mobile version