Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya ma wani Umarnin Shugaban Ƙasa na 11 hannu, wanda zai tabbatar da kula da ofisohsin gwamnati a faɗin Nijeriya.
Buhari ya sa hannu a kan dokar ne, gabanin fara zaman
Majalisar Zartarwa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Kafin ya sanya wa dokar hannu, Buhari ya nemi dukkan
ma’aikatun gwamnati’, da sashe-sashe da hukumomi su kafa
sashen kula da tafiyarwa a ƙarƙashin sabuwar dokar.
Bayan kammala sa hannun ne, shugaba Buhari ya jagoranci
zaman majalisar, wanda ministoci da sauran ƙusoshin gwamnati
su ka halarta.

