Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Buhari Bai Hana Ni Yin Takarar Shugaban Kasa Ba – Tinubu

Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari bai hana shi tsayawa takarar shugaban kasa yayin da shida ma shi burin shi na kokarin zama wanda zai gaje shi a shekara ta 2023 ba.

Tinubu ya ce batun neman shugabancin Nijeriya abu ne da ya jima ya na burin ganin ya cimmawa a rayuwar sa, sai dai ya ce har yanzu bai ya bayyana wa ‘yan Nijeriya muradin shi ba, ya na ci-gaba da tuntubar mutane don neman shawara.

Ya ce ya na da kwarin gwiwa da hange da kwarewar iya mulki da zai dora a kan turakun da shugaba Buhari ya kafa don sama wa Nijeriya makoma tagari.

Idan dai ba a manta ba, an dade ana rade-radin cewa Tinubu zai nemi takarar shugaban kasa, duba da yadda wasu kungiyoyi da fitattun mutane ke kokarin tallata shi a idon ‘yan Nijeriya.

Exit mobile version