Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bude Makarantu: Hukumar WAEC Da Gwamnati An Cimma Matsaya

Gwamnati Ba Ta Cire Dokar Hana Zirga-Zirga A Tsakanin Jihohi Ba

Gwamnatin Tarayya ta fara aikin sake gina makarantun da Boko Haram su ka ragargaza a Jihar Yobe da sauran sassan jihohin Arewa maso Gabas.

Gwamnatin tarayya da hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta yamma, sun cimma matsayar sauya ranar jarabawa.

A maimakon fara jarabawar a ranar 4 ga watan Augusta da ta sanar da farko, za a fara a ranar 5 ga watan Satumban 2020.

Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba

Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya sanar da hakan a Abuja, ya ce wannan ne sakamakon taron gwamnatin tarayya da shugabannin hukumar wanda suka gudanar.

Ministan ya kara da cewa, gwamnatin ta ba masu makarantu nan da ranar 29 ga watan Yulin 2020 don cika sharuddan bude makarantu.

Ya ce ma’aikatar tare da hadin guiwar ma’aikatar ilimi, hukumar yaki da cutuka masu yaduwa za su fitar da sharuddan bude makarantu.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi, Ben Bem Goong, a wata takarda, ya ce ana bukatar masu makarantun kudi da su shirya tare da bin dukkan ka’idojin.

Exit mobile version