Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bola Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fitar Da Gwani Na Shugaban Ƙasa Na APC

Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmad Tinubu, ya lashe zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar APC.

Tinubu Ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u dubu 1 da 271, kuma tun farko shi ne ‘yar manuniya ta nuna ya fi yawan ƙuri’u.

Bisa alƙaluman da aka sanar a bainar jama’a, ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu ƙuri’a 316, yayin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya samu ƙuri’a 235.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan kuma ya samu ƙuri’a 152, sau kuma gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ya samu ƙuri’a 47, tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha kuma bai samu ƙuri’a ko ɗaya ba, amma tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmad Sani Yariman Bakura ya samu
ƙuri’u hudu.

Tuni dai shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa Bola Tinubu tutar takarar shugabancin Nijeriya a karkashin jam’iyyar APC.

Exit mobile version