Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bashir Machina Ya Ce Ba Zai Janye Wa Sanata Ahmed Lawan Ba

Ɗan takarar Sanata na mazabar Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC Bashir Sheriff Machina, ya ce ya na iya zama shugaban majalisar dattawa nan gaba shi ma.

Yayin zantawa da manema labarai, Machina ya ce mutane su na ta tuntubar sa da sunan ya janye wa Sanata Ahmad Lawan, amma hakan ba mai yiwuwa ba ne.

Har yanzu dai ta na ƙasa ta na dabo game da makomar siyasar Sanata Ahmed Lawan, bayan ya rasa tikitin takarar shugaban ƙasa, kuma shekarun sa 15 ya na rike da kujerar Sanata na mazabar Yobe ta Arewa.

Bashir Machina, ya ce ya fitar da takardar da ya aike wa jam’iyyar a shafukan sada zumunta, game da tuntubar da aka yi ma shi ko ya na nan a kan takarar sa.

Ya ce shi dai bain janye ba kuma ba zai janye ba, ya na mai cewa Ahmed Lawan bai tuntube shi baki da baki ba, don haka ya na nan a kan bakan sa kamar yada jama’a su ka zaɓe shi.

Exit mobile version