Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bam Ya Raunata Kananan Yara 4 A Borno


Wani bam ya raunata yara hudu masu shekaru shida zuwa 10 a garin Ngala da ke Jihar Borno.

Yaran suna wasa a wajen gidansu da ke Ngala, sai suka ga wani bakon abu da ake zargin bam ne da mayakan ’yan Boko Haram suka harba a lokacin da suke rike da garin a baya, amma bai fashe ba.

Daya daga cikin yaran da bom din ya raunata ya ce, “Ban san ko mene ne ba.”

Wani jami’in wata kungiyar agaji ya ce, Yaran sun yi sha’awar sanin sa amma rashin dace da ban takaici da kuma  ban mamaki ya zama nakiya da ba ta fashe ba; Kafin su ankara sai ya tashi.

Fashewar wannan nakiya ta sa yaran suka samu munanan raunuka kuma nan take jirgin helikwafta na ICRC ya dauke su zuwa asibitin kwararru na jihar da ke Maiduguri.

Ya ce, yin amfani da makamai masu fashewa a wuraren da jama’a ke da yawa na iya haifar da illar da ba ta dace ba kuma yana da babban hadari ga jama’a.

Exit mobile version