Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ayyuka: Hanyar Abuja Zuwa Algeria Za Ta Kammala Cikin Shekaru Uku – Fashola

Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje

Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola, ya ce za a kammala hanyar da za ta hade Abuja da Birnin Algiers na kasar Algeria a cikin shekaru uku masu zuwa.

Duk da ya ke ya ce hanyar za ta ratsa kasashe irin su Nijar da Mali, hakan bai hana wasu sa shakku a lamarin ba.

A bangare daya dai wasu na cewa, a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Buhari ya kamata ta maida hankali a kan gyaran hanyoyin cikin gida da ke fama da ramuka, bai kamata a tada zance makamancin wancan ba.

A lokacin da ya ke magana da manema labarai, ministan ya ce ya kamata a nuna ba dukkan hanyoyin Nijeriya ke da muni ba, kuma hakkin ‘yan jarida ne su bayyana wa ‘yan Nijeriya cewa akwai aikin da a ke gudanarwa.

Exit mobile version