Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Aikin Hanyoyi: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Na’am Da Kashe Naira Biliyan 310

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Na’am Da Kashe Naira Biliyan 310

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Na’am Da Kashe Naira Biliyan 310

Yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke halartar taron majalisar dinkin Duniya, mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta kasa.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola

A zaman majalisar, Yemi Osinbajo ya amince da wasu kwangilolin tituna a fadin Nijeriya, wadanda za su ci kudi Naira biliyan 310.

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, ya bayyana wa manema labarai haka, jim kadan bayan kammala taron a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A cewar Ministan, majalisar zartarwa ta amince da Naira biliyan 79 na kudin da aka ware wa titin Ibada zuwa Ilesa da Ife, yayin da hanyar Asaba zuwa Garin Onitsha za ta ci akalla naira Biliyan 200.

A cikin ayyukan da aka amince da su, akwai hanyar Kano zuwa Katsina da aka ware wa Naira biliyan 29 da miliyan 65, kuma Kamfanin Julius Berger da Messrs Renold ne aka ba ayyukan.

Exit mobile version