Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Atiku Ya Sake Tabbatar Da Matakin Sa Na Tsayawa Takara

Atiku Abubakar

Atiku Abubakar

ya tabattar wa da cewa zai tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2027 duk da kalubalen da jam’iyyar sa ke fuskanta

Atiku Abubakar ya tabattar da hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha, a nan Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban kasan , karo na biyar kenan ya tsaya takarar shugaban kasa bayan dawowar Najeriya dimokraddiya

Ya kara da cewa ba zai ja da baya ba a tsayawa takarar shugaban kasa har tsawon iyakacin lokacin da Allah ya bashi karfi ko lafiya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma amince cewa ya wajabta jam’iyyar PDP ta hada gwiwa da wasu jam’iyyu idan har za ta kwato ragamar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.

Exit mobile version