Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

An Gano Manyan Jakunkuna Makare Da Kudade A Gidan Emefiele

Jami’an hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS, sun gano manyan
jakunkuna 18 makare da kudade da wasu takardu a gidan
dakataccen gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin
Emefiele.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa, hukumar DSS ta yi awon gaba da jakunkunan bayan ta dauki tsawon wuni guda ta na gudanar da bincike a gidan Emefiele da ke Lagos.

Kwanaki takwas kenan Emefiele na ci-gaba da kasancewa a hannun jami’an DSS, kuma bayanai na nuni da cewa akwai yiwuwar ya shafe ttsawonkwanaki nan gaba a hannun su, a daidai lokacin da ake ci-gaba da gudanar da bincike a kan badakalar da ake zargin shi da ita.

Yanzu haka dai hukumar DSS ta baza komar ta, tana neman wani mataimaki na musamman ga Emefiele ruwa a jallo, wanda aka ce shi ke rike da mukullan dukiya da kadarorin da tsohon gwamnan bankin ya mallaka ciki da wajen Nijeriya.

Exit mobile version