Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu Ta Umarci DSS Ta Bai Wa Emefiele Damar Ganin Lauyansa Da Iyalinsa

Wata babbar kotu da ke Abuja, ta umarci daraktan Hukumar
Tsaro ta Farin Kaya DSS Yusuf Bichi, ya ba dakataccen
gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele damar
ganin lauyoyin sa da iyalin sa.

Kotun a karkashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu, ta jaddada cewa ba Emefiele damar ya na cikin hakkin sa da kundin tsarin mulki ya ba shi.

Umrnin kotun dai ya biyo bayan bukatar da lauyan Emefiele J.B. Daudu ya shigar, inda ya ce hukumar DSS ta kasa amsa wasikun da aka rubuta a baya na neman samun damar ganawa da wanda ya ke karewa.

Lauyan Emefiele ya kara da cewa, hukumar DSS ta yi watsi da bukatun su a baya, sannan ta hana su ganawa da Emefiele, sai dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa hukumar tsaron za ta bi umarnin kotu, tare da ba lauyoyin da aka lissafa da iyalin sa damar ziyartar sa.

Tuni dai Kotun ta amince da bukatar, sannan ta dage sauraren karar zuwa ranar Talata, 19 ga watan Yuni na shekara ta 2023 domin ci-gaba da sauraren shari’ar.

Exit mobile version