Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra, ta ceto ‘yan mata akalla 35 daga wani otal da ke yankin Nkpor sakamakon wani samame da jami’an ta su ka kai, wurin da ake tilasta wa mata yin fasikanci domin su rika haihuwar jarirai ana saidawa.
Jami’an tsaron sun kai samamen ne tun ranar Litinin da ta gabata, a kan wani Otal mai suna Gally-Gally.
Yayin tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Anambra Tochukwu Ikenga, ya ce shekarun ‘yan matan da su ka ceto sun kama daga 14 zuwa 17, sannan hudu daga cikin su su na dauke da juna biyu.
Ikenga ya kara da cewa, ‘yan sanda sun kuma kwace bindigogi masu sarrafa kan su da dama, da tarin alburusai da kuma kudaden da yawan su ya kai naira dubu 877 da 500.
Kakakin ‘yan sandan, ya ce za su mika ‘yan matan da aka ceto ga hukumar hana safarar Bil-Adama ta kasa NAPTIP, yayin da masu laifin killace matan za su gurfana gaban kotu da zarar an kammala tatsar bayanai.

