Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Albishira: Ngige Ya Ce Gwamnatin Tarayya Za Ta Kara Wa Ma’aikata Albashi

Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma'aikatan gwamnati domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta.

Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta.

Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke nan Abuja.

Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ƙasa ya kafa na sake duba batun albashin ma’aikata, kuma ana sa ran zai zo da buƙatar ƙarin albashin a shekara mai kamawa.

Ministan kwadagon ya ce kwamitin na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar albashin ma’aikata ta ƙasa, dan haka yayin da aka shiga sabuwar shekara gwamnatin tarayya za ta ayyana batun ƙarin albashin.

Kan batun albashin wata takwas da malaman jami’o’in ke buƙatar gwamnati ta biya su kuwa, Ministan ya ce batun na gaban kotu.

Exit mobile version