Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ahmed Lawan Ya Karbi Kaddara Kan Hukuncin Kotun Da Ya Soke Takarar Sa

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce ya karbi hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya ce ba shi ne halastaccen dan takarar jam’iyyar APC a mazabar Yobe ta Arewa ba.

Matakin dai ya na zuwa ne, kwana guda bayan hukuncin kotun da ke zama a birnin Damaturu game da halastaccen dan takarar sanatan jam’iyyar APC na mazabar Yobe ta Arewa.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na yanar gizo, Sanata Ahmed Lawan ya ce bayan tuntubar abokan harkar siyasa da magoya baya da abokan arziki, yaa yanke shawarar ba zai daukaka kara a kan hukuncin ba, don haka ya karbi kaddara.

Sanarwar Sanatan dai ta kunshi wani bayani mai alamta yin ban-kwana, inda ya yi godiya ga shugabannin siyasar jihar Yobe da ma al’ummar mazabar sa, wadda ya wakilta tsawon shekaru a majalisun tarayya.

Exit mobile version