Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shugaba Buhari Ya Shilla Zuwa Kasar Afrika Ta Kudu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja zuwa kasar Afrika ta kudu.

Buhari dai zai kai ziyara kasar Afrika ta kudu ne, a kan rikicin kin jin baki da ya addabi kasar Afrika ta kudu a makonnin baya.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce shugaba Buhari zai tafi ne tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jiahr Kano, da gwamna Simon Lalong na jihar Plateau da kuma gwamna David Umahi na jihar Ebonyi.

Daga cikin ministocin su ka yi ma shi rakiya kuma akwai ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, da ministan tsaro Bashir Magashi da ministan lantarki Saleh Mamman, da ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, da kuma ministan ma’adinai Olamilekan Adegbite.

Sauran sun hada da ministan harkokin ‘yan sanda Maigari Dingyadi, da karamar ministar masana’antu, kasuwanci da hannun jari Mariam Katagum, da mai da shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Munguno, da shugaban hukumar liken asiri ta kasa Ahmed Rufai da shugabar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna ketare Abike Dabiri.

Exit mobile version